๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐: ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐
An taษa yin wani sarki a ฦasar Sin wanda ya bayar da umarnin a nemo masa dawakai masu iya yin gudun dubban kilomitoci a wuni guda ba tare da gajiyawa ba. Shekaru da dama aka shafe ana nema, amma ba a samu ba. Wata rana, wazirinsa ya zo ya shaida masa cewa an samo irin dawakan da yake nema. A take kuwa da jin hakan, ya biya kuษin su har kimanin sisin gwal dubu. Sai dai fa kash! Da aka kawo dawakan, sai aka tarar da su ba yadda Sarki ke nema ba, wato dawakai ne waษanda aka saba gani. Da sarki ya nuna rashin jin daษinsa, sai wazirin ya ce masa kada ya damu. Kamar dai yadda muka saba jin kaifin basirar wazirai, to shima wazirin nan ba'a bar sa a baya ba. Waziri ya bayyana ma Sarki cewa hikimar sa itace, biyan kuษi masu yawa kan dawakai na yau da kullum da yayi, zai sa mutane su fahimci girman burinsa, kuma idan aka samu na musamman (irin wanda yake nema), babu shakka shi za a fara kawo wa. Haka kuwa aka yi. Ba da daษewa ba, aka samo masa dawakan da suka zarce tsammaninsa. Wannan...