๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐: ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐
An taษa yin wani sarki a ฦasar Sin wanda ya bayar da umarnin a nemo masa dawakai masu iya yin gudun dubban kilomitoci a wuni guda ba tare da gajiyawa ba. Shekaru da dama aka shafe ana nema, amma ba a samu ba. Wata rana, wazirinsa ya zo ya shaida masa cewa an samo irin dawakan da yake nema. A take kuwa da jin hakan, ya biya kuษin su har kimanin sisin gwal dubu.
Sai dai fa kash! Da aka kawo dawakan, sai aka tarar da su ba yadda Sarki ke nema ba, wato dawakai ne waษanda aka saba gani. Da sarki ya nuna rashin jin daษinsa, sai wazirin ya ce masa kada ya damu.
Kamar dai yadda muka saba jin kaifin basirar wazirai, to shima wazirin nan ba'a bar sa a baya ba. Waziri ya bayyana ma Sarki cewa hikimar sa itace, biyan kuษi masu yawa kan dawakai na yau da kullum da yayi, zai sa mutane su fahimci girman burinsa, kuma idan aka samu na musamman (irin wanda yake nema), babu shakka shi za a fara kawo wa. Haka kuwa aka yi. Ba da daษewa ba, aka samo masa dawakan da suka zarce tsammaninsa.
Wannan na ษaya daga cikin tatsuniyoyin da ake bayarwa a nan Sin a irin wannan lokaci na sabuwar shekara ta dawaki. Ba wai don dawakan kawai ba, sai don darasin rayuwa da ke cikinsa: wani lokaci, girmama abin da wasu ke ganin ba shi da daraja (ฦananan abubuwa), na iya buษe ฦofa ga samun abin da ya fi daraja (manyan abubuwa).
Shi daman dai tsohon ciniki, duk wanda yazo yazo duniya fa iske shi yayi. Suma da alamu Sinawa a nan suma same shi. Tun asali, rayuwar Sinawa ta ginu ne a kan noma. Wannan ne ya sa suka danganta rayuwarsu da lokutan shekara da zagayowar yanayi. A sakamakon haka, tun ฦarni da dama da suka gabata, sun mallaki kalandar gargajiya mai watanni goma sha biyu (12).
Wadannan watanni goma sha biyu (12) ana ฦirgensu ne da dabbobi guda 12. Da zummar samun tasirin ko wace dabba a shekarar. Shi daman dai Suna aka ce linzami. To suma yaฦinin Sinawa kenan.
Abin lura a nan shi ne, wannan tsarin watanni goma sha biyu yana tuna mana abin da Al Qur’ani ya ambata cewa adadin watanni a wurin Allah goma sha biyu ne tun halittar sammai da ฦassai. Wannan na nuna yadda tun fil azal, al’ummomi daban-daban suka daษe suna lura da tsarin lokaci, kowa cikin fahimtarsa da al’adarsa.
Sabuwar shekarar Sinawa ita ce mafi girman balaguron ษan Adam a duniya. A wannan lokaci, fiye da mutane miliyon dubu ne ke komawa garuruwansu domin haษuwa da iyaye da iyalai da sabunta zumunci wanda suke fatan hakan zai zama ginshiฦin samun albarka a shekara mai farawa.
A dalilin haka ne ake dakatar da duk wani aiki na ฦwadago. Duk da irin yadda Sinawa ke da hazaฦa a aiki da neman kuษi (ฦila Kanawa suce basu kai su ba). Ko ina ana tafiya hutu, hatta kasuwanni, abin da ke nuna irin muhimmancin iyali a rayuwarsu.
Kamar yadda al'ummu keda chamfe-chamfe, Sinawa ma ba'a bar su a baya ba. A tunani na ma ba mamaki su shiga cikin jerin manyan masu imani da chamfe chamfe a duniya.
Daga cikin chamfe chamfen su akwai tsabtace gida gaba ษaya kadin jajibiri, domin kada a shiga sabuwar shekara da tarkacen baya. Haka kuma, ana amfani da jajayen kaya da harba wasan wuta (fireworks), waษanda suka samo asali daga tatsuniyar wani dodo mai zuwa idan anyi girbin amfanin gona mai suna "Nian ๅนด" (wanda ke nufin Shekara a yaren su), wanda ake cewa yana tsoron ฦara mai ฦarfi da kuma launin ja.
Wannan shekarar ta 2026 kuwa, a kalandar gargajiyar Sinawa, ita ce Shekarar Dawaki. Hakan ya tunaman da shekarar giwaye ta labarawa, amma banbanci da lissafin Sinawa shine yana maimaituwa, su kuma labarawa dalilin wani abu ne da ya faru kawai. A fahimtar Sinawa, doki alama ce ta ฦarfi, sauri da nasara. Wannan ne ya sa sabuwar shekararsu ke zuwa da fata na samun ci gaba mai sauri kamar gudun doki mai nisa, irin wadanda wancan sarkin ya samu. Gaishe gaishe da rabon kyaututtuka sun cika ko ina a Birnin Sin.
Ga musulman da ke zaune a Sin kuwa, wannan lokaci ya zo da wata dama ta musamman, domin ya yi daidai da watan Ramalana, wanda hakan zai ba da dama ga wasu su fara azumi tare da iyalansu cikin natsuwa.
A yau, yayin da Sin ke ci gaba da taka muhimmiyar rawa a duniya, irin waษannan al’adu na nuna yadda suke haษa tarihi da zamani, kamar yadda jagoran Sinawa da masu zaman cirani (su ฦanlami) ya bayyana a saฦon da ya aika na sabuwar shekara, wurin nasu cigaban.
Kallo kuwa na nan a wannan shekara idan da rai da lafiya, duba da yanayin canjin akalar siyasar duniya da ake samu, musamman ganin ziyarce ziyarcen da shuwagabannin kanada da birtaniyya suka kawo birnin Sin a kwanakin baya.
Wannan shi ne yanayin rayuwa daga nan kusa da bangon duniya.
Allah Ya ba mu ikon isa watan Ramalana cikin aminci, Allah Ya kuma sa mu yi ibada karษaษษiya.
Ameen.
๐๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐ ๐๐ฌ๐ฆ๐๐ง
Daga Birnin Sin,
Kusa da Bangon Duniya.

Comments
Post a Comment